Ad

Breaking News

Jam’iyyar PDP zata lashe zaben 2019 – David Mark

– Tsohon shugaban majalisar Dattawan Najeriya, David Mark, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP zata lashe zaben 2019
– Ya nemi jam’iyyar ta tsaida yan takara nagari domin ta sake samun damar mulkin Tarayyar Najeriya
Sanata david mark
Sanata David mark a lokacin daya ziyarci Agatu
Sanata David mark, tsohon shugaban majalisar Dattawan Najeriya, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP zata lashe zaben da za’a gudanar a 2019.
Sanata Mark ya bayyana cewa tilasta zaben yan takara da akayi a 2015 ne ya sanya jam’iyyar PDP ta fadi zabe kuma mulkin shekarun ta sixteen yazo karshe saboda wannan kuskuren knowledge aikata.
Inda yake magantawa da mutane a Otukpo, Sanata Mark ya bayyana cewa dole PDP ta hanu daga dauki daura da take yima yan takara domin ta samu mulki a 2019.
Yace “Dole mu bude idanun mu akan cewa dauki daura da shugabanni suke yi wajen kawo dan takara ya sanya PDP ta fadi zabe a 2015.
“Yanzu komai ya fito karara. Kowa yaga banbancin. Don haka dole PDP ta sanya mutanen kirki domin shugabanci jam’iyyar zuwa nasara a 2019.
Ya bayyana cewa jam’iyar nada yiyuwaer dawowa kan mulki idan duka mambobin jam’iyyar sukayi aiki domin talakan Najeriya.
Taron ya samu halarci daga Abba Moro, tsohon Ministan cikin gida a lokacin Jonathan, Emmanuel Agbo, Geoffrey Ejiga da sauran wasu manyan baki wadanda aka gayyata.
Idan za’a iya tunawa, kimanin watanni 2 ke nan da jam’iyyar PDP ta nada Sanata Ali Modu Sherif, tsohon gwamman Jihar Borno a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar.
Wannan ne ya sanya wasu daga cikin mambobin kungiyar sukayi fushi inda ake zargin cewa suna shirin fita daga jam’iyyar ne domin kokarin kafa tasu.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin shi zata cigaba da dukkanin wasu alkawurra da gwamnatin Jonathan ta shiga da kasar China. Shugaba Buhari ya bayyana wannan ne a jiya kafin ya tashi zuwa kasar domin ziyara ta kwanaki four.
The publish Jam’iyyar PDP zata lashe zaben 2019 – David Mark appeared first on Nigeria Information immediately & Breaking information | Learn on NAIJ.COM.